Masoyin Fatima Yayi Tattaki Daga Zariya Zuwa Sokoto Domin Duba Lafiyarta.


Masoyin Fatima Yayi Tattaki Daga Zariya Zuwa Sokoto Domin Duba Lafiyarta.

Kamar Yadda Muka wallafa labarin Ismail Basawa, Mai Sana'ar Kafinta  Dan Asalin Garin Zariya,  Wanda Yayi Alkawarin Auren Fatima, Wacce taga mu da Ibtla'i na Rasa Kafarta Tuni Ismail yayi Tattataki Daga Garin Zariya Zuwa Garin Sokoto A wanan Rana Domin Zuwa Duba Lafiyar Masoyiyar sa  Fatima,  Da Kuma Tattaunawa da iyayenta.

Fatima, Tayi Farin Cikin Da Ziyarar da Ya Kawo Mata da Kuma Kaunar da ya nuna Mata Suma iyayen Fatima Sun nuna jin dadinsu bisa Kaunar 'Yar su da Ya nuna da kuma Tausayawa Bisa ibtala'in da yafaru da ita A Karshe sunyi Masa Addu'ar In matar sa ce Allah ya tabbatar da Alkhairi.

A nasa bangaren Ismail basawa, Ya Godewa Yan Jarida bisa kokarin isar da Sakon da Sukayi har takai ga Sun Hadu da Fatima Fuska da fuska
Previous Post Next Post